Kungiyar y'an kasuwar hatsi da kayan abinci ta Dawanau a Karamar Hukumar Dawakin Tofa a jihar Kano ta dauki matakan kare kasuwar ta hanyar daukar masu gadi 800 aiki.
Shugaban kungiyar yan kasuwar, Alhaji Muntaka Isa ne ya bayyana hakan ga kamfanin dillancin labarai na kasa NAN a yau Litinin.
Ya bayyana irin kokarin da gamayayyar jami'an yan sanda da sojoji suka yi wajen tabbatar da tsaro a jihar.
Ya kara da cewa sun kara daukar masu gadi 400 wadanda ke aiki tare da jami'an tsaro wajen bada kariya ga kasuwar.
Acewarsa, kasuwar ta fuskanci barazana daga bata gari daga unguwannin Kurna da Bachirawa wadanda suka yi yunkurin afkawa a yayin zanga- zanga.