Yanzu-yanzu: An aikewa majalisar dokoki takardar neman rushe Masarautu hudu da dawo da Muhammadu Sunusi 2 Sarkin Kano

 Yanzu haka wata kungiya mai suna “Yan Dangwalen Jihar Kano” ta rubutawa majalisar dokokin jihar Kano takardar neman rushe dokar kafa karin masarautu hudu da suka hadar da Gaya, Rano, Karaye da Bichi, wadanda gwamnatin da ta gabata ta kafa, tare da neman a maido da Sarkin Kano na 14 Mallam Muhammadu Sanusi II.



Bayanin kungiyar na zuwa ne ta cikin wata wasika mai kwanan watan Fabrairu 5, 2024, da aike wa kakakin majalisar dokokin jihar Kano, inda ta ce rusa masarautu tare da maido da Muhammadu Sanusi na biyu a matsayin sarkin Kano “zai samar da hadin kai, zaman lafiya da kwanciyar hankali a fadin jihar Kano

Previous Post Next Post