Malami Ibrahim Daurawa ya sauka daga mukamin shugaban Hisba ta Kano Buyo bayan Gwamnan Kano Abba Gidagida

 Bayan irin abubuwan da suke faruwa akan irin ayyukan da hukumar hisbah take karkarshin kwamanda Sheikh Aminu Ibrahim daurawa na operation dauka badala inda ake ta kamo mata da maza da sauransu wanda abubuwan ba’a cewa komai.



Babban kamun da yafi daga hankali al’umma shine kama wata fitacciyar yar tiktok murja kunya wanda nan take hisbah na kai ta kotu daga nan anka sake ta, bayan korafi da yayi yawa sai anka sake kama ta.


Daga nan gwamnan jihar kano engr Abba Kabir Yusuf yayi magana acewa akwai Kurakurai akan ayyukan da hukumar ita hisbah keyi, wanda a yau din nan mun samu sakon sauka daga mukami daga bakin shehin malami Sheikh Aminu Ibrahim daurawa wanda shine kwamandan hisbah.

Previous Post Next Post