Yanzu – Yanzu : kotun koli ta tabbatar da Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamnan kano

 Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf na Jam’iyyar NNPP ya isa harabar Kotun ƙoli da za ta yanke hukunci kan ƙarar da ya ɗaukaka don ƙalubalantar hukuncin kotun ɗaukaka ƙara da ta soke nasararsa.



Gwamna Abba Kabir yana ƙalubalantar hukuncin ne bayan da ƙananan hotuna suka bai wa tsohon mataimakin gwamnan Kano, Nasiru Yusuf Gawuna nasara.


Tun da farko, kotun zaɓen gwamnan Kano a watan Satumban 2023 ce ta soke ƙuri’a 165,633 wadda in ji ta, aka yi wa ɗan takarar na jam’iyyar NNPP aringizo, bayan hukumar zaɓe a watan Maris, ta ce ya samu ƙuri’a 1,019, 602.

Previous Post Next Post