Matsalar Saurin Inzali Da Yadda Za'a Magance Ta

 inzali gabansa ya ke kwantawa ba,to zai raka ta kadan yana kaiwa yana komowa har itama ta biya bukatar ta.




Sai dai dole ne ango ya lura da inda yafi sa matarsa jin dadi don kuwa matan sun sha bambam. Inda zaka tabawa wata ta ji dadi ba lalle ne in ka tabawa wata za ta ji dadi ba.




2. Nesantar Da Al'aurarsa Daga Jikinta.


Idan har mutum na da saurin inzali,to yayin da suke wasa shi kuwa sai ya guji goga gabansa a jikinta hakanan kuma ita matar kar ta yi masa wasan. Ma'ana kar ta shafa ko taba gabansa har yayin da za su sadu.




3. Tsayawa Yayin Da Ake Jima'i.


A yayin da suke jima'i idan ya ji alamar zai yi inzali sai su dakata da abin da suke, hakan ya hada da daina motsi zuwa wani lokaci har sai ya ji ya koma, sai su ci gaba. Haka zai dinga yi har sai ya ga alamar ita kuma za tayi inzalin sai su yi tare ko ma ta riga shi. Saboda da wannan dalilin ne muka ambata a baya cewa al'amarin na bukatar hadin kan ma'auratan a junan su.




4. Motsa Jiki.


Bincike ya tabbatar da cewa motsa jiki da ya hada da sassarfa, gudu, da sauran wasannin motsa jiki na taimakawa mai wannan matsala ya samu waraka.




5. Yanayin Kwanciya Lokacin Saduwa.


Yadda ma'aurata za su kwanta na da tasiri ta fuskar inzali. Bincike ya nuna amarya ta hau kan ango zai bayu zuwa ga saurin kawowarta. Ka ga idan haka ne, to lalle irin wannan kwanciya za ta taimakawa mai saurin inzali.


Shi ma wannan yana bukatar a gwada, idan an dace, to an samu mafita.




6. Jan Nunfashi Sannan A Sake Shi.


Mun fada a sama cewa dakatawa na kara tsawon lokacin kawowa. Hakanan a yayin da ake cikin jima'i sai a ja nunfashi ta hanci sosai ya shiga cikin ciki, sai a sake shi a hankali. Wannan ma na kawo jinkirin inzali.




7. Yin Jima'i A Hankali.


A guji gaggawa a yayin da ake jima'i da iyali. Abin nufi yayin da namiji ke kaiwa da komowa a kan iyali to yayi hakan a hankali,don kuwa zuwa da dawowa da saurin kan haifar da inzali ba tare da ka shirya ba.




Muna fata masu fama da wannan matsala za su jarraba bin wadannan hanyoyi don samu waraka daga wannan matsala mai tarwatsa rayuwar aure, kuma muna addu'a Allah Ya sa sanadiyar mu


ne za su samu kubuta daga wannan matsala,amin.

Previous Post Next Post