MASHA ALLAH Zuwaira Ahmad: ‘Yar Shekara 13 Da Ta Rubuta Alqur’ani Da Ka

 MASHA ALLAH Zuwaira Ahmad: 'Yar Shekara 13 Da Ta Rubuta Alqur'ani Da Ka

Yarinyar mai suna Zuwaira Ahmad daliba ce a Makarantar Madrasatu Tahfizil Kur'an Waddirasatil Islamiyya da ke kauyen Kagara a Karamar Hukumar Kafur a Jihar Katsina inda aka ce ta rubuta cikakken Kur'ani Mai girma a cikin wata biyu.

Malama Zuwaira ta fara rubutu na biyu a ranar Litinin da ta wuce, inda take fatar kammalawa cikin kankanin lokaci.

Abin da ya shagaltar da ni da kuma natsuwa gaba daya a halin yanzu shi ne karatu da rubuta Alkur'ani Mai girma kuma babban burina shi ne in ga cewa na samu ilimi mai yawa kuma mutane da yawa su amfana da abin da na samu," inji ta. 

An shigar da Zuwaira makarantar Islamiyya a kauyensu Kagara, tana da shekara bakwai, inji mahaifinta, Malam Ahmad Ibrahim Kagara, inda ta haddace Alkur'ani a cikin shekara shida.

"Yau tana da shekara 13 da wata hudu, mun shigar da ita tana da shekara bakwai da wata uku, duk abin da ta samu ta fuskar hadda da rubuta Alkur'ani Mai girma tana makaranta daya ba ta taba zuwa wata makarantar ba.

"Muna matukar godiya ga Allah Madaukakin Sarki yayin da ta rubuta Alkur'ani a cikin wata biyu da 'yan kwanaki. Da ta yi sauri fiye da haka idan ban da mukan nemi ta huta sau daya," inji shi. 

ne karatu da rubuta Alkur'ani Mai girma kuma babban burina shi ne in ga cewa na samu ilimi mai yawa kuma mutane da yawa su amfana da abin da na samu," inji ta.

An shigar da Zuwaira makarantar Islamiyya a kauyensu Kagara, tana da shekara bakwai, inji mahaifinta, Malam Ahmad Ibrahim Kagara, inda ta haddace Alkur'ani a cikin shekara shida.

"Yau tana da shekara 13 da wata hudu, mun shigar da ita tana da shekara bakwai da wata uku, duk abin da ta samu ta fuskar hadda da rubuta Alkur'ani Mai girma tana makaranta daya ba ta taba zuwa wata makarantar ba.

"Muna matukar godiya ga Allah Madaukakin Sarki yayin da ta rubuta Alkur'ani a cikin wata biyu da 'yan kwanaki. Da ta yi sauri fiye da haka idan ban da mukan nemi ta huta sau daya," inji shi.

Previous Post Next Post