Duk wanda zai aure ni, to dole ya kori Mamansa a gidansa: Cewar Khadija

 Khadijah wata matashiya ce da ta yi kaurin suna a shafin sada zumunta na Tuwita, inda sunan shafin ta da kowa ya sani shine 00deejatoubea, to a yanzu haka ta fito ta bayyana irin ka’ida da mijin da zai aure ta zai bi.


Cikin wani sako da ta wallafa a shafin nata na Tuwita, ta bayyana cewa matukar za ta yi aure, to dole mijinta ya tabbatar da cewa mamanshi ba za ta zauna a gidansu ba har na kwana uku.

“Duk wanda zai aure ni, to dole ya amince da ka’idata cewa mamansa ba za ta zauna a gidan da za mu zauna ba har na fiye da tsawon kwana uku, Maganar Gaskiya kenan”

Ko da yake ba ta bayyana irin dalilinta na yin haka ba, to amma jama’a da dama sun yi sharhi kan wannan batu nata inda wani bangare mai girman gaske na ganin abin nata azimun ne.

Ita dai Khadijah matashiya ce wacce da ganinta ka san son kowa ce ƙin wanda ya rasa, wata kila hakan ne wasu ke ganin ya sanya ta wannan aika-aika.

Duk da cewa dai shafin Tuwita a yanzu haka ma vi gana da daukar zafi ko wane wayewar gari, to amma jama’a da dama ma’abota shafin, na wallafa bayanai ne don raha.


Ko da yake daga bisani kamar matashiyar ta goge rubutun nata bayan ganin ruwan maganganu masu dadi da akasin haka, amma rubutun ya janyo cece-cece cuki da wajen tuwita.

To ko ma dai da wasa take yi, lamarin zaman uwar miji a gidan danta na zama wa matan wannan zamani tamkar karfen kafa ne, inda har tuni da ma suka sa mata suna da Olsa (Ulcer).

Previous Post Next Post