Budurwa Ta Siyawa Me Gadinta Takalmin 👞 Naira Miliyan 1 Dan Yasa Yaje Masallacin Juma'a. Me Zaku'iya Cewa..?

 Shahararriyar mai zanen nan, kuma tsohuwar budurwar shugaban kungiyar direbobi ta Legas MC Olumo, wato Ehi Ogbebor, ta gwangwanje mai gadinta da takalma kirar 'Louis Vuitton' da ta saya akan kudi Dalar Amurka 1000 kwatankwacin Naira Miliyan daya da doriya.



Karamcin da Ehi Ogbebor ta yi wa mai gadin nata ta haifar da ce-ce-ku-ce a yanar gizo inda wasu ke cewa kamata yayi ta bashi kudin a maimakon ta siya masa wannan takalmin mai dan karen tsada.

Previous Post Next Post