An garzaya da wani magidanci asibiti, bayan da ya sha maganin karfin maza, gabansa ya ki kwantawa duk da kokarin ’yan uwa da abokan arziki na shawo kan al’amarin.
Wani kwararren ma’aikacin jinya a Asibitin Kwararru na Sakkwato, Ibrahim Abdullahi, ya ce, saura kiris a yanke shawarar yi wa mutumin tiyata a gabansa, domin sai da suka shafe kwana uku suna jinyar mutumin kafin gaban nasa ya kwanta.