Masoya kance so hana ganin laifi labarin wata budurwa da ta tattara inata inata tabar gidansu da ke sabuwar kofa ta tare a gidansu saurayinta a garin yakasai da ke jihar kano da ake arewacin najeriya.
Gidan rediyo Freedom Radio kano ne sunka samu tattaunawa da wannan budurwa inda yanzu haka ta shafe da kwana sama da dari 100 a gidansu saurayin tana rayuwa da kanensa inda daya daga cikin ma’aikatan Freedom Radio kano ya zanta da wannan saurayi.
“Tun farkon haduwar mu da wannan yarinya,yara suke tsokar ta, nayi ruwa nayi tsaki to a nan taga itafa taga miji a nan ne fa na zaunar da ita ina koya mata yadda zata iya magana a cikin al’umma , nan ne tace tana sona amma ban bata amsar hakan ba.
Nan take cewa shin zaka aure, sai nace mata shi aure nufi ne na Allah– inji saurayi.”
A nan ne fa wannan budurwa tayi fatali da kunyar malam bahaushe ta zamo mishi bita zaizai, nan ne take gayawa walikin freedom Radio kano cewa ita guguwar soyayya ce ta dibeta, amma tace kada mutane suga laifinta domin ko wace zuciya tana son mai kyautata mata har take karanto wani hadisi.
“Ina son shi sosai kuma iyayena sun san da ina son shi da zan samu auren gata da shi da zanji daɗi.
Inaso a taimaka aka auramin shi domin ta dalilinsa ne na kasa samun natsuwa da sukuni, domin idan ban ganshi ba, bana jin dadi a cikin zuciyata- inji budurwa.”
Kiran budurwa mai soyayya ga mutane.
“Da su taimaka su aura min shi”
A cikin rahoton kuma abba saidu sufi shine babban daraktan hukumar hisbah a jihar kano yace zasu gayyato waɗanda masoya har da iyayensu domin a samu mafita.
” A dauko wannan yarinya a kawo wannan hukuma kuma za’a nemi iyayenta duk abinda ya kamata in aure za’a yi musu za’a sasu ayi musu aure wata Allah in rabasu za’ayi, za’a samu in ma Shari’a za’a yi musu hukumar hisbah za’a bincika“- inji Abba sufi.