Allah Sarki Mutane da dama Sun Jinjinawa Abba gida gida bayan da Yakai Ziyarar bazata Wajen Karamar Yarinya dake Neman Taimako a Asibiti.

 Allah Sarki Mutane da dama Sun Jinjinawa Abba gida gida bayan da Yakai Ziyarar bazata Wajen Karamar Yarinya dake Neman Taimako a Asibiti.


Mutane da dama Sun Jinjinawa Abba gida gida bayan da Yakai Wata Ziyarar bazata Wajen wata Karamar Yarinya da Sauran Marasa lafiya dake Neman Taimako a Asibiti dala ta Jahar Kano.

Gwamnan Jahar Kano Abba Kabir Yusuf Yakai wata Ziyarar bazata a Asibitin orthopedic dake dala domin duba wata Karamar Yarinya hade da sauran Marasa lafiya a Asibitin. 

Mai girma Gwamnan Kano Abba Kabir Yusuf Ya Wallafa a Shafinsa na Facebook Kamar Haka Naga anata Wallafa Hotunan wata Karamar Yarinya Asmau a Kafafen Sada Zumunta ana Neman Taimako Wanda Hakan ya dauki hankalina kuma na dauki lokaci na ziyarce ta da sauran marasa lafiya a Asibitin Orthopedic dake a Dala.



Mun biya Mata Kudi Naira miliyan 1.5 Kudin Magani da sauran abubuwa. Za Kuma Muci gaba da sanya ido akan Lamarin ta domin ganin ta samu lafiya da sauran marasa lafiya a jiharmu.


Ga Cikakken Bidiyon Ziyarar da Yakai nan Kamar haka.

Previous Post Next Post