Adam Kamaye Ta Bayyana Dalilin Da Yasa Aka Yanke Mata Hukunchi Kisa A Saudiya Da Kuma Kubutar Da Tayi

 danna na’ura, ta yi ƙara. Ina buɗewa sai ga jami’an tsaro birjik.”


Adama ta ce a nan aka tarkata dukkan matan da ke cikin ɗakin, aka yi ƙasa da su, har su takwas.


Laifin Da Ya Janyo Aka Yanke Mana Hukuncin Kisa’ – Adamar Kamaye:


Adama ta shaida wa Hadiza Gabon cewa ba ta san laifin da ta yi ba, sai ga su tsare a kurkuku har su takwas. Ta ce a can ne aka kulle su cikin ɗaki ɗaya, kuma aka haɗa su da wasu jami’an tsaron su amma masu jin Hausa.


Ta ce su na wannan zama ne dai ta riƙa cewa ita dai an zalunce ta, ba ta san laifin da aka yi ba.


“To a nan ne ƙawar tawa ta ce min gaskiya ke ba ki yi laifi ba, kin dai taka sawun ɓarawo ne kawai”.


Yadda Ƙawa Ta Ta Tsara Kisan Wani Dattijon Balaraben Da Ta Ke Aiki A Gidan Sa’ – Adamar Kamaye:


Adama ta ce ƙawar ta ashe ta yi aiki a gidan wani dattijon Balarabe har ta shirya yadda aka kashe shi, aka kwashe maƙudan kuɗaɗe da gwala-gwalai, bayan tsawon rabuwar da ta yi da ita.


Ta ce, “An ɗauki ƙawar tawa aiki a gidan wani dattijon Balarabe, wanda ba ya iya ko tafiya, sai dai komai a kan keken guragu. To ita ce ke hidimar kula da shi.


“Wannan dattijo ya na da ‘ya’ya maza uku, kuma dukkan su matuƙa jiragen sama ne.


Duk wata sukan aiko masa da kuɗaɗe masu yawa a cikin kata-katan. To sai ƙawa ta ta shirya ita da wasu ƙawayen ta yadda za su sace kuɗaɗen.


“Wata rana matar dattijon ya tafi biki a Riyad, sai ƙawa ta ɗin ta kira wasu ƙawayen ta, ta ce su zo su kwashe kuɗin.


“Da su ka je sai suka wuce ɗakin da ake ajiyar kuɗin, su ka kwashe duka.”


Adama ta ce bayan ɓarayin sun fice, sai dattijon ya ce wa ƙawar ta, ya aka yi ɓarayin su ka samu makullin gidan har suka buɗe su ka shiga?


A nan dai sai ƙawa ta kira ɓarayin ta ce to tsohon nan fa ya gane. Shi ne sai suka koma su ka ɗaure shi a kan kujerar keken da yake a zaune. Suka toshe masa baki da addugar amfanin mata lokacin al’ada, duk aka gudu har da ƙawar tawa.”



Adama ta ce wannan laifin ne ya sa aka biyo sawun su a daidai ranar da ita ma Adama ta je gidan waɗanda suka aikata laifin.


Ta ce asirin waɗanda su ka yi kisan tonu, ta hanyar mai aikin makullin da ƙawar ta ta kai aka yanka mata wani safaya. Ta ce shi ne ya bayar da shaidar cewa tabbas a rana kaza ‘yar aikin gidan mamacin ta je wajen sa ta kai makulli ya yanka mata.


Adama ta ce a ƙarshe dai ita an sallame ta, amma sauran su bakwai duk an yanke masu hukuncin kisa.

Previous Post Next Post