Ango Ya Saki Bidiyon Abinda Ya Faru Tsakaninsa Da Matarsa A Daren Farko

 Wani Ango ne dai ya saki Amaryarsa saki daya a daren da aka kawota tun kafin ya shiga ɗakin.


Hakan dai ya biyo bayan da kawayen Amaryar ne suka kulle kofa suka ce sam bazasu bude kofar dakin ba sai an biyasu kudin al'ada ta sayen baki har naira dubu dari biyu (#200,000).


Da jin haka sai abokan Ango suka yi ta luguden labba da kawayen Amaryar don neman ayi musu sassauci. Bayan da Angon yaga abin ya ki ci kuma ya ki cinyewa ga dare na kara tsawo ana bata lokaci tunda kawayen sun kafe kan sai an biya #200,000 yaga dai da gaske sukeyi, sai yace a basu naira dubu talatin (#30,000).

Bayan an kidayo dubu talatin aka ce gashi su bude kofar sai kawai kawayen Amaryar suka kekasa kasa suka ce basu yarda ba, naira dubu talatin (#30,000) tayi kadan. Don haka ba zasu


bude kofar ba sai an karo.

Daga nan sai Angon ya kira Amaryarsa a waya sau biyu, ita kuma taki daga wayar Angonta.


Abinka da kaddara, aikuwa cikin fushi sai Angon ya dauki wayarsa ya turawa Amaryarsa sakon karta-kwana wato (Text Message), cewa, 'Na sakeki saki daya.


Kafın kace kwabo! Kawayen sun bude kofar kowa ta gudu gidansu suka bar Amarya da Sallallami cikin bakin ciki.



Previous Post Next Post