Amarya ta kashe angonta a daren farko

 Yau a cikin garin Bauchi a wata unguwa da ake kira Dumi wata mata ta halaka mijinta ta hanyar caka masa wukã suka uku a kirjinsa



Zuwa yanzu dai babu wanda yasan dalilin da yasa ta kâshe mijinta, zanje State CID Bauchi na bi diddigin dalilin da yasa wannan yarinya ta káshe mijinta na aure.


Abin takaici, da wahala kaji miji ya kashé matarsa, yawanci sai dai a ji mata ta kashe mijinta.

Maza ku dinga sanin irin matan da zaku aura ta hanyar nazari da karantar halayyarsu idan suna cikin bacin rai


Mafi kololuwar laifi a tsakanin ma’aurata shine miji yazo ya tarar da kwarto a kan matarsa, ko mata tazo ta tarar da mijinta akan kwartuwa, ba duka ba zagi, a rabu kawai rabuwa na har abada, Allah Zai yi sakayya


Zaman aure ba dole bane, shiyasa Allah Ya halasta rabuwa idan akwai cutuwa, cin amana, zargi ko zalunci a tsakanin ma’aurata

Previous Post Next Post