Malamina Yana Sauke Alkur'ani A Kasa Da Rabin Awa (30minutes)- Sheikh Prof Makari

 Mataimakin babban limamin Babban Masallacin Abuja, Sheikh, Farfesa Ibrahim Makari ya bayyana cewa Malaminsa yana sauke Alkur'ani mai cikin kasa da rabin awa.



Fitaccen malamin ya faɗi haka ne a cikin wani faifan bidiyo, inda yake magana kan irin baiwa da karamar da Allah Ya ba Malaminsa. Duk da cewa bai ambata sunan malamin nasa ba, amma ya ce yana daya daga cikin mafi kusa da shi.




Malamin ya nuna cewa wasu za su yi mamaki a ce wani ya sauke Alkur'ani a kasa da minti 30, to amma a cewarsa, wannan ba abin mamaki ba ne ga wanda Allah Ya hore ma wa.

Previous Post Next Post