Yadda Yin Tallah Ga ‘Yam Mata Yake Tasiri Wajen Lalata Rayuwarsu

 Kaman yanda natakaita managar a shafina nace talla ya zama bara zana ga ƴaran mata yanzu, musanman masu sayar da abinci, gyaɗan, pure water, masa, kwankwa mati, ƙwai, kuli kuli, dama rauran su.



Wasu iyayen suna sakawa ƴaran mata talla ne saboda su nima abin da za su ci kuma su kara rufa ma Kan su asiri saboda babu yanda za suyi, amma ana samu wasu iyayen suna sakawa ƴaran su talla ne saboda son abin duniya alhalin Allah ya rufa masu asiri babu shakka wannan babban kuskuri ne ga iyaye mata


Watarana kusan sau uku ina ganin ana zubar da “masa” a bayan gidan mu abin ya sha bani mamaki ina “tambayan” kai na shin wa yake wannan aikin? ya zubar da “masa” masu kyau alhalin bai lalace ba, sai wani lokaci nafito daga gida misalin karfe goma na safe sai nayi ido biyu da mai wannan aikin ashe wata ƴar talla ce idan aka bata talla sai ta zubar da shi, kuma ba karaman yarinya ce ba budurwa ce take wannan aikin. sai na “tambaye ta” ko me dalili idan aka baki talla kina zubar da shi? sai tace ai wani Alhaji ne yana mani juye kullu idan nafito wurin sa nake zuwa sai ya min juye kuma yakara bar mani “masan” shi yasa nake zubar da shi domin kuwa idan bai kare ba mamana sai tayi mani kukan tsiya, sai abin ya bani mamaki da tace wani Alhaji ne yana yi mata juye kullu


Da yawa iyaye mata suna kuskure ki baiwa yarinya talla kice kar ki yarda ki dawo da wani abu agidan nan sai ya kare wannan kuskuri ne babban saboda wannan kalma yana iya sa yarinya ta fa ɗi daga sherrin zina saboda tana tsoron kar ta dawo da wani abu, tana iya bayar da kan ta domin ta samu kuɗin da zata baiwa wace ta bata talla gudun kar ta sha dukan tsiya.

Wani lokaci ina tunani ko ƴara da ake basu talla kaman ba iyayen su ba ne, ƴaƴan goyo ne, domin nata ƴaƴan suna makaranta suna karatu sabado ba za ta yarda nata ƴaƴan suyi talla ba amma ita za ta baiwa ƴaƴan wasu talla. yana da kyau kusawa ƴaƴan ku ido agidan goyo


Kuma kaman yanda na faɗa a baya talla illace ga yaa mace a wurin talla ce idon yarinya yake buɗe saboda tana hurda da maza iri iri kuma a wajen ne ƴan isaka suke zama ka gani lalacewa mai sauki ne, kuwa a wajen ƴan iska ko da kuwa kina da tarbiya sun san yanda za suyi su ɓata maki rayuwa Allah ya kyauta.


Sau da yawa ƴara da a kafi masu fyde ƴan talla ne mafi akasarin cikin su ƴan talla ne, Allah ya kyauta


Yana da kyau amasayin ka na uba kasa idanuwa ƙwarai da gaske akan ƴaƴan ka, ganin ka basu tarbiya da ilimi kuma har in dai kafi karfin abin da za ka ci kar ka yarda ka bari ƴaƴan ka suna talla ko da kuwa suna gidan iyayen ka ne,


Yaa Allah ka worewa kowa yafi karfin abin da zai ci na yau da kullun.

Previous Post Next Post