Dalilin da yasa matasan jihar Kano suke son Abba Kabir Yusuf Inkiya Abba Gida Gida ya zama gwabnan Kano.
Daga Ibrahim Adam.
Matasan Kano suna son Abba Gida Gida ne saboda suna da yakinin cewa tsarin da yake kai zai dawo da harkar kai 'yan uwansu matasa karatu, wannan tsari ne da ake yinsa don matasa su samu ilimi ingantacce ta hanyar kaisu makarantu daban daban a sassan duniya domin su samu kwarewa a ilimi da gogewar rayuwa.
Za'a dawo da tsarin tallafawa matasa ta hanyar basu jari da kuma tallafawa wanda suke da rauni a sana'arsu domin habaka sana'ar. Wannan tsarin an yishi a gwabnatin Kwankwasiyya a baya ku
a sana'arsu domin habaka sana'ar. Wannan tsarin an yishi a gwabnatin Kwankwasiyya a baya kuma shine tsarin da Abba Gida Gida zai dora akai.
Haka zalika, za'a dawo da harkar kiwon lafiya, wanda haihuwa yake kyauta a asibitoci tare da bayar da ingantaccen kulawa ga marasa lafiya.
Dadi da kari, mata a gida za'a dawo da tsarin ba su jari domin fara kananan sana'u da ake yinsu daga gidaje. Wannan duk abubuwa ne da gwabnatin Kwankwasiyya ta yi a baya kuma matasa na da yakinin cewa idan Abba Gida Gida ya zama gwabnan jihar Kano, za'a cigaba da wadannan tsarika.

Matasa na son zuwan Abba Gida Gida saboda kannensu 'yan makaranta (musamman mata). Za'a dawo da motocin da suke sufurin kaiwa da kawowa wajen kai kannensu makaranta, dawo da tsarin raba kayan makaranta da sauran abubuwan bukatun dalibai don inganta walwalar