Ana muhawara kan kalaman Ganduje na 'rashin sanin wanda zai mika wa mulki
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje
A jihar Kano da ke arewacin Najeriya, ana takaddama a fagen siyasa, bayan gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya ce ba shi da tabbaci kan jam'iyyar da zai mika wa mulki.
Ya bayyana haka ne duk da kasancewar babbar jam'iyyar adawa ta NNPP ce hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta ayyana a matsayin wadda ta lashe zaben gwamnan jihar.
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya bayyana haka ne, yayin da ya ke kaddamar da daya daga cikin hanyoyin da gwamnatinsa ta samar a cikin birnin Kano, inda ya ce Allah ne kadai ya san jam'iyyar da zai mika wa mulki a ranar 20 ga watan Mayun 2023.
Ya ce "Mun kirkiro manya-manyan ayyuka, mun kammala wasu ba mu kammala wasu ba, wanda ba mu iya kammala su ba muna fatan gwamnati mai zuwa ko gwamnati NNPP ko kuma ta APC, Allah ne kawai Ya sani. Mu na rokon su su cigaba da abin da su ka tarar."
Ana muhawara kan kalaman Ganduje na 'rashin sanin wanda zai mika wa mulki
Jam'iyyar APC ta gwamna Abdullahi Ganduje dai ta sha kayi ne a zaben gwamnan jihar da aka gudanar ranar 18 ga watan Maris, a zaben wanda ya yi zafi tsakanin yan takara biyu da ke samun goyon bayan iyayen gida na siyasar jihar.
Tuni dai jam'iyyar APC ta gabatar da korafi domin bin kadin sakamakon zaben.