Hukumar Kididdiga ta Nijeriya, (NBS) ta bayyana jihohin Legas, Ogun da Kano a matsayin wadanda suka fi yawan masu amfani da wayar salula, da kuma masu amfani da intanet.
A wani rahoto da ta saba fitarwa duk bayan watanni uku, NBS ta yi bayani kan harkokin tarho, wanda ya kunshi bayanai na watannin ukun karshe na shekarar 2022.
Bayanan sun hada da na adadin masu kiran waya, da masu amfani da intanet, da kuma yawan masu amfani da kowane kamfanin sadarwar da ke kasar.
A cikin rahoton, a watannin karshen 2022, jimillar mutanen da suka yi kiran wayar salula ta kai 222,571,568. Sai kuma jimillar wadanda suka yi amfani da intanet da ta kai 154,847,901.
Jihohin da ke kan gaba da kuma na karshe a amfani da salula da data
Jihar Legas da ke kudu masu yammacin kasar ce ke kan gaba a yawan masu amfani da salula, mai biye mata ita ce makwabciyarta jihar Ogun, sai kuma Kano da ke arewa maso yammaci, a mataki na uku.
Ga jerin jihohi uku da ke kan gaba da kuma na matakin karshe a watannin karshen 2022:
Mataki JIHA Amfani da kiran salula Amfani da data
Ta daya Legas 26,460,867 18,702,394
Ta biyu Ogun 12,994,352 9,206,614
Ta uku Kano 12,373,201 8,470,131
Ta talatin da biyar Ekiti 2,001,846 1,474,970
Ta talatin da shida Ebonyi 1,920,996 1,264,825
Ta talatin da bakwai Bayelsa 1,571,692 1,101,002
A bangaren kamfanonin salula da ke Nijeriya, a karshen 2022, kamfanin MTN ne ya fi yawan masu yin kiran salula, wadanda suka kai 89,016,678, da kuam masu amfani da data da suka kai 65,619,610.