Allahu Akbar Allah Ya Karbi Rayuwar ta a Yayinda take Tsaka da Sallah Allah Ta’ala Ya gafarta Mata

 Ƙanwata marigayiya Maryam tana da ƙyawawan ɗabi’un da ake buƙata ga ’Ya mace har a iya fahimtar cewa wancan mace ne na ƙwarai (Mai riƙo da addini)‚ ga girmama manya ko batasanka ba‚ tausaya ma yara Ɗalibanta sun mata wannan shedan‚ marigayiya Maryam Tsahon sanina da ita ban taɓa jinta da kowa ba‚ ban taɓa jin wani ya kawo ƙarar ta kan wani laifi da tayi ba‚ saidai a yabeta akan ƙyawawan halayenta.



Jiya Daren Talata 17/04/2023 wanda yai daidai da 26 ga Ramadan‚ 1444H. Marigayiya Maryam lafiya lau ta uni‚ har Allah ta’ala ya bata ikon azumtar inin ranar‚ bayan shan ruwa tayi buɗa baki tare da gabatar da sallolin ta na farali‚ ta gabatar da Sallah na Ashman kamar yadda ta saba‚ Ashe sallar ƙarshe ne‚ tana kan Sallayan bata tashi da ƙafar ta ba sai gawan ta a ɗauka Allah ta’ala ya amshi rayuwar ’Yar’uwata Maryam. Inna ilaihi wa inna ilaihi raji’un! Ƙanwata Maryam ta rasu tabar wannan gidan duniya har abada baza ta dawo ba.

Duk mai rai mamacine iya dare daɗewa. Amma mutuwar lokaci ɗaya akwai sosa zuciya musamman ace rasuwar Budurwa mai son ganin goben yara tayi kyau‚ mai ƙoƙarin gaske wajan karatu da karantarwa‚ mutuwar irinsu akwai girgiza me tsanani. Abin fata ne ga dukkan al’ummar musulmi ace sun mutu (Sun koma ga Allah ta’ala) irin mutuwar wannan baiwar Allah. Ta rasu a watan Ramadan‚ daɗin daɗawa saida ta sauke faralin da Allah ta’ala ya wajabta mata na wannan inin‚ harta ƙara da nafiloli sallamar ta na ƙarshe yayin ganawanta da Ubangijin talikai Allah ta’ala ya amshi rayuwar ta.

Wannan ƙarshe ne mai kyau da kowa da kowa yake fatan ya yi irin sa. Allah yasa hashashenmu akanki na samun gidan Aljanna ya tabbata a gareki da sauran bayi na gari‚ Allah ya amsheki a matsayin Shahida. In Sha Allah kinyi dacen zuwa barzak ’Yar’uwa. Anyi mata Sutura Kamar yadda addinin musulunci ya koyar‚ a binne ta a makwacinta da safiyar yau ɗin nan.

Previous Post Next Post