Yadda Wani Matashi Ya Harbe Kaninsa Yayin Gwada Maganin Bindiga

 A wani lamari mai cike abin jimami da ya auku a jihar Kwara inda wani matashi ya halaka kanin sa yayin gwada maganin bindiga kamar yadda Jaridar Labarun 


Hausa ta rawaito.

Matashin mai suna Abubakar Abubakar ya harbi kanin sa har lahira mai suna Yusuf Abubakar dan shekara 12, domin gwada ingancin sabon maganin bindigan da suka siyo. Jaridar Daily Trust ta rahoto.


Mahaifin yaron matashi yana da bindigar farauta


Abubakar mamacin yayan wani mafarauci ne a karamar hukumar Kaiama ta jihar Kwara.


An samo cewa lamarin ya auku ne a ranar Lahadi, sannan matashin Abubakar yayi batan dabo tun bayan aukuwar lamarin. Ya gudu ne bayan ya aikata wannan danyen aikin.

yaron matashi ya dauko bindigar farauta ta mahaifin sa sannan ya harbi kanin sa, maganin bai yi aiki ba wanda nan take matashi Yusuf ya rasu a wurin.


Okasanmi ya shawarci iyaye da su rika sa ido kan abubuwan da yaran su ke aikatawa.


Yakamata su dai na yin abubuwan da ba su dace ba domin hana aukuwar irin wannan lamarin a nan gaba, a cewar kakakin yan sandan.

Previous Post Next Post