Tofah! Safara’u Ta Magantu Akan Fitar Bidiyonta Daya Janyo Cece Kuce

 Lallai akwai babbar illa ga tarbiyar yara mata lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su. ‘Yan mata da yawa sun fada fikin gurbacewar tarbiya lokacin da suka bukaci yin aure aka hana su. Wani lokaci yara mata kan bukaci yuin aure, amma sai iyayesu su hana su, ko don saboda karatu ko wanda suka kawo su iyayen ba sa san su ko kuma saboda wadanda dalilai, wannan ba karamar raunata tarbiyar yuara mata ya ke yi ba. Sakamakon hakan, sai ka ga sun fada shaye-shaye, karuwanci da kuma wasu hanyoyi wadanda ba su dace ba.

 


An samu wata yarinya da ta bukaci mahaifinta ya yi mata aure, kuma har ma ta kawo wanda ta ke so, amma mahaifin nan yaki, daga karshe yarinyar ta rubuta masa wasika cewa, “na tafi idan ka zo sai Allah ya yi mana shari’a.” Sai ta hau saman bene, inda ta fado ta mutu har lahira. Haka kuma, wata ta samu mahaifinta ta bayyana masa cewa, ya yi mata aure ko kuma ta lalace ta bi duniya. Idan za a samu irin wannan lamari, to ya kamata iyaye su tashi daga barcin da suke yi wajen aurar da yaransu lokacin da suka bukata. Koda mahaifin nan bai da kudin aurar da diyarsa, ya kamata ya kira wanda ta kawo masa a matsayin wanda ta ke ta aura idan har mutumin kirki ne, to sai ya zauna da shi ya bayayyana masa cewa, shi fa bai da kudi, ya kawo abin da ya sauwaka sai a daura musu aure.

 

Lallai iyaye su sani Allah zai tambayesu hakkin yaransu ranar alkiyama, su daina cutar da yaransu wajen hana su aure lokacin da suke bukata, domin ba su san yadda suke ji ba. Idan hai ‘ya mace za ta iya tunkarar mahaifinta a kan ya yi mata aure, to lalle tura ta kai bango. Ya kamata iyaye su dunga jin tausayin ‘ya’yansu wajen tashin hankali da suke samu lokacin da sha’awa ta same su. Ba dai-dai ba ne a ce, iyaye sun yi sanadiyyar lalacewar yaransu wanda Allah ya ba su amana.

Daga karshe ina kira ga iyaye su rage san abun duniya, domin ya kare wa ya bar ka ko kuma mutum ya kare ya bar abun duniya. Kwadayin sai ‘ya’ya mata sun kammala karatun boko kifin aure, wannan ba dilili ba ne. A auran da mace idan mijinta ya bari ta ci gaba da karatu, to sai ta ci gaba, idan kuma ya ki yarda, to sai a bar ta da wanna ta samu tare da rokon Allah ya sa masa albarka. Ina fatan iyaye za su amfana da wannan karamar shawarata da kuma yin amfani da ita na barin yaransu su yi aure a lokacin da suke bukata.

Previous Post Next Post