suke tsira daga kirjin mace da zaran ta soma
balaga, ma’ana fitowarsa yana cikin alamomin
balaga na mata. Bayaga halitta ne da Mahalicci yayi domin alamta
balaga ga mace, har ila yau yana cikin alamomin
dake bambamta jinsi na mace dana namiji, domin
duk macen data haura munzalin balaga kuma
akaga cewa babu wani tsiro na nonuwa daga
kirjinta ya zama matsala. Haka nan namijin da duk aka ganshi da nonuwa a kirjinsa tamkar mace, to
ansan da matsala. Haka kuma nonuwan dama yafi
na hagu tsayi na kowace mace.
Haka nan kuma Allah Ya halicci nonuwa a jikinki
mace ne domin ta samu wajen adana abincin jinjirin
da zata haifa, ganin ruwan nonuwan mace shine abincin da jinjiri yake iya amfani dashi a matsayin
abinci na wani lokaci mai tsawo kamin ya soma cin
wani abinci mai nauyi.
Har ila yau shine abu na farko dake bayyanar da
kyau ‘ya mace da zaran sun soma fita daga kirjinta
kuma suka kai munjalin girmansu. Don haka nema masana kwalliya da kyele-kyele suke cewa macen
datake da cikenken nonuwa tafi kyau idan tayi
kwalliya fiye da wacce bata da cikan kirji. Anan
manufa shine baya ga abubuwan da muka ambata
a baya, nonuwan mace suna da da kawata mata
kyaunta fiye da mara shi. A bangaren jima’i kuma, nonuwan mace yana
dauke da kusan kashi 35 wajen samar da dadin
dake cikinsa, domin idan kika kasa mata kashi 100,
70 daga cikinsu sha’awarsu na saurin motsawa ne
da zaran anyi musu wasa da nonuwansu. Tabbasa
da wadannan dalilan kadai ba zamu ga cewa, nonuwa a jikin mace ba karamin hikima da baiwa
Allah Yayi a halittansu ba, don haka ya zama dole
ga mata su bi duk wata hanyar da zasu bi na halas
domin ganin cewa suna kula dasu