Nifa a halin yanzu da ka bani kyautar Naira Miliyan 5 gara ka aureni-Hauwa'u Abdullahi

 Kamar dai yadda kuka sani yan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.


Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.



Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers. ta yadda za kuga yan mata da samari na yin abubuwan da zasu dauki hankulan abokansu na sada zumunta.


Wata budurwa mai suna Hauwa'u Abdullahi mai lakabin Jiddarh a shafinta na Twitter ta bayyana wa Duniya cewa ita fa a halin da ake ciki yanzu da bata kyautar Naira miliyan biyar kwara a aureta kamar yadda zaku ga hoton Screenshot din rubutunta daga kasa.

Previous Post Next Post