Nifa ba Tarbiyya Nazo Koyarwa ba a Kannywood Kudi Kawai Nazo Nema Cewar Jarumi Sadiq Sani Sadiq

 Fitaccen Jarumi a Masana’antar Kannywood Sadiq Sani Sadiq Ya bayyana cewa shifa ba Tarbiyya Yazo Koyarwa ba a Kannywood Kawai kudinsa yake nema a wata hira da akayi dashi a kafar yada labarai ta freedom radio kano.


Kamar dai yadda aka sani fitaccen Malamin Addinin Musuluncin nan Watau Sheikh Idris Abdulazeez bauchi ya kalubalenci Yan Masana’antar shirya Finafinan Hausa akan cewa kaf dinsu babu me Ilimin Addini Acikinsu duk jahilaine.


Wanda hakan ne ya tayar da cece kuce harma wasu daga cikin jaruman Kannywood suka maida masa Zazzafan martani akan maganarsa wanda daga cikin su akwai jarumi sadiq sani sadiq wanda ya bayyana cewa yana fatan ya mutu yaje ga Allah a matsayin dan Fim.

Sai dai Kuma daga baya yayi nadamar abinda ya furta hakan yasa yanzu ya bayyana cewa shifa dama ba Tarbiyya Yazo Koyarwa ba a Kannywood Kudin shi kawai yazo nema.


kalli cikakken vedion anan


Previous Post Next Post