A karshe dai gani tare da iyayen Hauwa'u da kayayyakin dauka saya musu daga gudummawa da bayin Allah suka bayar
wanda jimillarsa ya kama naira dubu ɗari takwas da arba'in da bakwai da naira dari biyu da tamanin (N847,280.00).
Abubuwan Da aka saya sune kamar haka:-
1. Gado
2. Katifa
3. Complete set na kujeru
4. Labule (curtain)
5. Ledar tsakar daki yadi goma
6. Kayan kitchen complete
7. Bed sheet
8. Turmi na daka
9. Food flask, flates, spoons da sauransu.
10. Buhun shinkafa guda 2 guda 1 za'a hada
mata a cikin kayan gara, sauran guda 1
kuma iyayenta za suyi amfani da ita a
gidansu.
.Haka zalika tunda aure za'a yiwa Hauwa'u
mun mata tanadi na musamman domin dogaro Da kanta a gidan miji, mun saya mata kaya kamar haka:-
1. Keken Dɗnki
2. Awakai guda 4 Maza 2 Mata 2 Domin kiwo 3.Sai naira dubu Hamsin N50,000 (50k) za'a sayi itace ta dinga siyarwa a gida Duk dai saboda taci gaba da kulawa da kanta.
Itama mahaifiyarta an bata dubu Hamsin
A bangaren mahaifinta kuwa shima ya rabauta da naira dubu hamsin (50k) domin yaci gaba Da sana'arsa ta fruits da ya daina yi sakamakon rashin jari. A farko munyi niyyar bashi dubu 100 ne amman sakamakon mun fahimci gidansa yana bukatar yan gyare-gyare sai muka bashi dubu hamsin ya kara jarin, sauran dubu hamsin din da sauran kudin da ya rage za muyi amfani dasu wajen gyara musu bandaki, dakin girki, rijiya da wani bangare.
Total kudin furnitures, Katifa, ledar tsakar daki N346,500.
Total kudin keken dinki, Awakai, shinkafa buhu 2 labulaye Da Sauransu N210,500.
Transport cost N22,000.
Mun cika N43,000 Mun sayi sauran kayan Kitchen saboda akwai wata baiwar Allah data bamu wasu daga ciki.
Total kudin da aka vawa Hauwa'u da iyayenta da sauran 50k Da za'ayi musu gyara ya kama dubu dari takwas da goma N832,000.00.
Kudin da ya rage 25,280.00 sune zamu hada da sauran dubun hamsin ɗin da muka ware domin gyara wani bangare na cikin gidansu kamar yadda nayi bayani a sama.
Mun ja hankalin saurayinta wanda shine zata Aura da yayi kokari ya rike Hauwa'u da Amana, kuma ya kara tsaya mata taci gaba da zuwa makarantar Islamiyyar data saba zuwa tunda matan Aure ma suna zuwa.
A karshe ina jinjina da godiya ta musamman ga wadanda suka bada gudunmowa ta kudi, wasu daga cikin kayan kitchen, shawarwari da addu'a, Allah ya sakawa kowa da alkhairi,
Allah ya biya mana dukkan bukatunmu na alkhairi. x