Kyawawan hotunan Sarkin Kano Da Kyakkyawar Amaryarsa

 A yau Juma’a ne aka ɗaura auren Mai Martaba Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero da amaryarsa Hauwa’u Adamu Abdullahi Dikko da aka fi sani da Hajiyayye.



Majiya mai tushe ta bayyana cewa an dade ana kwasar soyayya tsakanin Mai Martaba Sarkin Kano da Amaryar tasa tun kafin ya zama Sarkin Kano na 15 a ranar 11 ga Maris, 2022.

Kafin wannan auren, Mai Martaba Sarkin Kano, yana da mata daya ne da suka kwashe sama da shekara 30 da kuma 'ya'ya hudu, sabanin yadda aka saba gani a tsakanin Sarakuna. 

An ɗaura auren ne a gidan marigayi Jarman Kano, Farfesa Isah Hashim da ke unguwar Nassarawa a birnin Kano, ba tare da halartar mutane da yawa ba.

Madakin Kano Alhaji Yusuf Nabahani Cigari, shi ne ya kasance wakilin Mai Martaba Sarkin Kano, yayin da Alhaji Shehu Hashim ya yi waliccin Amarya, kamar yadda jaridar Manhaja ta ruwaito.
Majiyarmu ta ce tun a shekarar da ta gabata aka yi baikon basaraken da amaryarsa, inda sai a wannan lokaci aka ɗaura auren.

An ce amaryar zuri’ar marigayi Malam Jamo ne, wanda ɗan'uwa yake ga marigayi Sarkin Kano na biyu a daular Sarakunan Fulani Malam Ibrahim Dabo.

Daga cikin waɗanda suka halarci ɗaurin auren sun haɗa da Makaman Bichi, Alhaji Isyaku Umar Tofa da Sarkin Dawaki Mai Tuta na Kano, Alhaji Bello Abubakar Tuta da Ɗan Ruwatan Ringim da sauransu.



Previous Post Next Post