Ko Gobe Ruwa Na Maganin Dauda Domin Har Yanzu Ana Yayina A Kannywood Fati - Bararoji

 A Wata tattaunawa da akayi da tsohuwar jaruma a masana'antar shirya Fina-finan ta Kannywood Fati Baffa Fagge, wacce akafi Sani da Fati Bararoji.


Bararoji Ta bayyana cewar ita fa har yanzu batayi tsufan da za a daina yayin ta ba acikin masana'antar Kannywood domin kuwa, har yanzu a na damawa da ita kamar lokacin kuruciyar ta.

Duk da cewa girma ya fara kamata amma duk da hakan jarumar ta bayyana cewa ko gobe ruwa na maganin dauda, ma'ana har yanzu ana yayinsu lokacinsu na haskawa.

Previous Post Next Post