Kalli Yadda Jaruma Nafisat Abdullahi tayi Shagalin Bikin Ranar Zagayowar Haihuwar ta a wani Kayataccen Wuri Mai daukar Hankali.

 Kalli Yadda Jaruma Nafisat Abdullahi tayi Shagalin Bikin Ranar Zagayowar Haihuwar ta a wani Kayataccen Wuri Mai daukar Hankali.



Fitacciyar Jaruma a Masana’antar shirya Finafinan Hausa Nafisat Abdullahi Wacce akafi sani da Sumayya Acikin Shiri me dogon zango labarina.


Ta gudanar da Shagalin Bikin Ranar Zagayowar Haihuwar ta a wani Kayataccen Wuri Me matukar daukar Hankali….. Jarumar dai tana daya daga cikin manyan jaruman Kannywood kuma fitattun yan Kasuwa Wanda a yanzu haka tana da kampanin siyar sa kayan Kwalliya na zamani wanda tasa masa suna Nafs costimetics.


Jarumar dama ta saba Gabatar da irin wannan Shagalin biki a duk Shekara, sai dai a wannan Karon kuma yanayin taron Shagalin bikin ya bawa mutane mamaki kasancewar babu wani dan Masana’antar Kannywood da aka gani a wurin illa wasu tsurarun mutane da ba’a sansu ba.

An bayyana cewa jarumar ta gayyaci iyakacin yan uwanta ne wanda basu wuce mutum biyar ba.

Mutane da dama sun tayata murna kowa kuma ya tofa albarkacin bakinsa inda har wani yayi mata martani cewa ke anata mutuwa amma kinzo kina hoto koh?


A yayinda jarumar ta mayar masa da cewa Ai kowa zai mutu dan haka ya kwantar da hankalinsa, sannan kuma rashin posting ba shine zai dawo mata da Mahaifiyar ta data rasu ba.


A karshe jarumar tayi godiya ga daukacin Masoyan ta da suka tayata da murnar wannan babbar rana a gareta.



Previous Post Next Post