Ina samun Naira Miliyan daya da rabi a duk Mako a sana'ar Carbin Malam - Inji Ramatu

 An sami wata mata a kauyen Fadima da ke da tazarar kilo mita 6 daga babban birnin Katsina, wadda ba a taba samun yar kasuwa mai himma kamarta ba a kauyen.



Fadima wani garin Hausa-Fulani ne da ke kan titin Katsina zuwa Kano, kafın ka kai garin Eka. Babbar sana'arsu ita ce noma da kiwon dabbobi.

Ramatu, wata matar aure mai matsakaicin shekaru, wadda kuma ba ta yi karatun boko ba, ta fara sana'ar alewar carbin malan bayan aurenta na fari wanda bai jima sosai ba


Ramatu ta yi jawabi dalla-dalla a game da nasarar da ta samu a cikin sana'arta ta alewar carbin malam.


Ramatu ta ce: "Innata ce ta shigar da ni cikin wannan kasuwancin. Ita ce ta koyar da ni duk abin da na sani da kuma yadda ake hada alewar gargajiyar."


Za ka yi matukar mamaki a gidan Ramatu idan ka ga yadda ma'aikata sama da 70, ciki har da yara mata da maza, suke aikin hada alewar da A kunshe ta cikin sauri da kwarewa.

Bayan ta gama koya, sai Ramatu ta fara gudanar da sana'ar a karon farko da sikarin naira 400 da kwakwa guda daya. Bayan ta gama hadawa sai ta kai carbin malam din wata kasuwa da ke kusa da su domin ta sayar. A haka ta cigaba da sana'ar, amma sai kasuwancin ya karye sakamakon rashin ciniki da karancin kudi a hannunta.


"Ba wata riba na dinga samu ba a farko. Na sha wahala sosai domin na dinga faduwa amma na cigaba da jajircewa."

Ta ci gaba da cewa, "A lokacin mahaifiyata da kakata suka ki taimaka min da bashin wasu kudi domin in farfado da sana'ata. Da na ga ba yadda zanyi sai na sayar da kayan dakina na aure sannan nayi amfani da kudin gurin farfado da sana'ata da ta karye." Inji ta


Bayan shekaru biyar da zuba kudin kayan dakinta a sana'ar, sai Allah ya sanya albarka a ciki har ta kai ta kere innarta da ta koya mata sana'ar a kafuwa.


Da aka tambaye ta a kan nawa take samu a dukkan rana, sai ta ce, "Ina samun naira dubu dari biyu a kullum."


Ta kara da fadin cewa, "Ina siyan buhuna 13 na sikari a kullum.

Hakan na nufin kenan Ramatu na siyan sama da buhuna 91 na sikari a duk sati. Bayan nan tana samun ribar naira miliyan 1.4, shi ma a kowanne sati.


A yanzu haka tana sayar da carbin malan dinta a dukkan kananan hukumomi 34 na jihar Katsina da ma sauran makwabtan jihohi.


A kokarinta na sama wa matasa mata da maza na kauyenta aiki, Ramatu ta dauki ma'aikata sama da 80 aiki. Da yawan ma'aikatan nata matasa ne yan tsakanin shekara 14 zuwa 25. A yanzu haka ta fadada kasuwarta zuwa jihohin Kano, Kaduna da Legas.

Yusuf Iro, mazaunin kauyen Fadima ne, ya bayyana cewa ana kai carbin malam din Ramatu wasu bangarorin kudancin Najeriya.


Safiya, wata ma'aikaciyar Ramatu, ta ce, "Tun da na fara aiki da ita, ban kara tambayar iyayena kudi ba. Ina amfani da kudin da nake samu gurin biyan kudin makarantana da na yan uwana."


Ita ma A'isha, yar shekara 20, ta bayyana cewa sam yanzu ba ta damun iyayenta a kan su ba ta kudi. Tana amfanin da kudin da take samu gurin ciyar da iyayenta da kuma biyan kudin makaranta.

Kazalika kowanne ma'aikaci yana samun akalla sama da naira 500 zuwa 3000 a rana, amma kudin ya dogara da yawan kullin da ka iya hadawa.


Ramatu ta bayyana cewa ita burinta shi ne ta tallafa wa yara mata da fasahar da za ta taimaka musu gurin samun dan kudin da za su rufa wa kansu asiri.


Daga karshe ta ce babban kalubalen da take fuskanta shine tsadar kudin sikari, saboda haka take rokon gwamnati ta sanya tallafi a kai domin ta samu damar kara yawan sikarin da take saya. Ta ce hakan zai taimaka mata gurin kara samun riba da kuma diban karin ma'aikata.

Previous Post Next Post