Wannan photon da kuke gani photon wani rami ne dake cikin wata Sahara a kasar Turkmenistan.
Wani abin al'ajabi ya faru a kasar Turkmenistan wanda ya dauki hankalin hukumomin kasar dama sauran al'umma a fadin kasar wanda kuma masu zuwa yawon bude ido suke tururuwa don ganewa idonsu na wani ramin da ake kyautata zaton gabar wutar jahannama ce.
Wannan ramin da kuke gani an bayyana cewar ya shefe kimanin shekaru 5,000 yana ci da wuta, kuma duk ruwan saman da ake tafkawa a tsawon shekaru da iska basa taba kashe wannan wutar ba.
Wurin wannan ramin yana daya daga cikin guraren da sukafi bawa Duniya mamaki inda yake daukar hankali na masu sha'awar yawon bude ido.
Wutar ance tana ci fiye da shekara 5,000 kuma har yanzu bata mutu ba babu kuma wani alamun da ke nuna cewar zata lafa don kuwa ko gezau bata yi ballentana ta mutu.
Wannan waje ne da dubban mutane sukan je daga kasashe daban daban domin gani, har wasu da dama suke cewa Kofar Wutar Jahannama ce, wacce take dauke da wasu abubuwa na ban mamaki wanda hakan yasa aka koma kiran wajen da suna "Gate of Hell" ko kuma "Door of Hell".