Daga Dandalin Twitter
Kamar dai yadda kuka sani yan mata da samari na baje kolinsu a shafukan sada zumunta na zamani wato Social Media.
Inda wasu ke amfani da kafafen na sada zumunta irin su Facebook, Twitter, Instagram, da dai sauransu wajen gudanar da harakokin da suka shafi kasuwanci.
Wasu kuma ke yin rubuce-rubuce da nufin jan hankalin mabiyansu wato followers, ta yadda za kuga yan mata da samari na yin abubuwan da zasu dauki hankulan abokansu na sada zumunta.
Wata matashiya da ke zama daya daga cikin masu amfani da shafin Twitter ta yi wani rubutu wanda ya dauki hankalin mabiyanta kamar haka, "Misali ace maza su kona haihuwa, nawa kike so mijinki ya haifa miki? yasin sai ya haifa min yaya 20 sannan zan bar shi ya huta" in ji ta.