Bidiyon So Baya Da Kama: Hotunan Wasu Masoya Sun Dauki Hankula Sosai

 Daga Aisha Ibrahim Gezawa


Bidiyon wani saurayi da budurwar sa wacce ta kasance wada ce ya dauki hankula sosai. Daga sanya daukar har sama da mutum duba dari uku sun kalla a manhajar TikTok.

A cikin bidiyon wanda Martin Edotse, ya sanya, an ga saurayin cikin izza yana nunawa duniya kyakkyawar budurwar sa.


Masoyan biyu dai farin ciki ya bayyana matuka a fuskokin su a cikin bidiyon mai tsawon dakika 9 wanda aka sanya a dandalin sada zumunta.


Masu amfani da kafar TikTok bidiyon yayi matukar birge su inda ya karade manhajar. Ba a samu tabbacin cewa ko masoyan biyu sun yi aure ba, amma mutane da dama a wajen yin sharhi sun yi tunanin cewa sun yi aure.

Wasu mutanen na ganin cewar da ace budurwar itace namijin da kaji mutane nata yekuwar cewa mata da kudi. Mutane da dama sun yi martani bayan ganin bidiyan ma'auratan.

Previous Post Next Post