Wani shafin twitter mai suna 'FADILA
ZANNAH' da ya yi kaurin suna a kwananan sakamakon sanarwar da mai shafin
tayi/yayi na cewa, tana neman mijin
aure, to a zahiri namiji ne (Gardi) mai
shafin ba mace ba.
Wannan shafi dai na 'Fadila Zannah' ana zargin wani mutum ne ya bude da nufin neman jama'a, da za su bibiyi shafin ta kafar sadarwa.
Tuni dai rahotanni sun ce wanda ya aikata wannan mummunar dabi'a wanda mazaunin Kano ne, ya shiga hannun jami'an tsaro.
Bayanai sun tabbatar da cewa, shi dai wanda ake zargin, ya dauki hotunan wata baiwar Allah ne mai suna "Samira Sulaiman Saje" sannan ya bude shafin
Sulaiman Saje" sannan ya bude shafin twitter din da suna na bogi, 'Fadila Zannah'
Dan uwa ga "Samira Sulaiman Saje, Kabiru Sulaiman Saje" wanda shine ya yi ruwa yayi tsaki wajen binciko batagarin da yayi amfani da hotunan kanwartasa, ya bude shafi a twitter, ya shaidawa "Gaskiya Ta Fi Kwabo" cewa, iyalan gidansu sun shiga mawuyacin hali bayan da suka samu labarin hotunan kanwarsu na yawo a kafafen sadarwa da sunan wai tana neman mijin aure.
"Shi mutumin (batagarin), yana bibiyar kanwata Samira a Instagram, saboda haka aduk lokacin da ta sanya sabbin hotuna a Instagram sai ya sauke a wayarsa"
"Da wadannan hotunan yayi amfani ya
bude shafin bogi mai suna 'Fadila Zannah' saboda ya rika damfarar maza marasa tarbiyya " inji Kabiru Saje".