Cikin wani bidiyo mai cike da tausayi wata mata mai suna Maria da bata da kafafu da hannaye ya dauki hankali duniya kwarai da gaske bayan da Afrimax ta wallafa bidiyon.
Bidiyon da shafin YouTube na Afrimax
English ya sanya shekarar da ta gabata ya samu makallata kusan Miliyan daya da rabi, ya nuna yadda matar take rayuwa.
Matar mai suna Maria yar shekaru 20, ta shaida irin halin kunci da tsangwama da suke fuskanta daga mutanen gari, ta kuma nuna yadda talauci ke mata barazana ita da iyalanta.
Maria ta ce ita tana ganin wannan nakasar da take ita tamkar gado sukeyi, domin kuwa bayan ita dan da ta haifa shima a haka yake, kafarsa da hannunsa sun zo bai guda.
Zaku iya kallon cikakkiyar tattaunawar da tashar Afrimax
English tayi da wannan mata.
https://youtu.be/cND_Ted1Fg4