Matar Aure Takai Mijinta Kotu Saboda Yana Kwana Tsirara Ba Wando

 Wani Bidiyo Daya Dauki Hankali A Shafin Tiktok Kuma Abun Dariya Na Yadda Wata Mata Takai Mijinta Kotu Bisa Abunda Yake Yi Mata Batajin Dadi Yana Kwana Babu Wando.


Rohoton Da Labarai.com.ng Suka Wallafa Matar da aka bukaci a sakaye sunanta ta kai Mijin nata Kotu ne akan baya kwana da wando,zuwa gurin Alkalin keda wuya Mijin yaga ai an riga an gama kunyata shi a idon duniya,daya rasa mai zai fada sai kawai yace “Ya Mai Girma Mai Shari’a! Ai fitsarin kwance take yimin kulllum nayi-nayi ta dena taki,ni kuma na gaji da shanyar wando ko idan na fita in dinga zarni” a cewar Mijin.
Rufe bakinsa keda wuya ta dora hannu aka tana ihu, Mijinta ya gama da kunyata ta a idon duniya.

Labarin ya fito ne daga bakin Malam Lawan Triumph,ga bidiyon domin ku kalla.

A Wani Bangaren Kuma
“Namiji Dan Goyo ne” Shawarar Wata Mata Ga Matan Yanzu
NAMIJI ‘DAN GOYO NE GA WADDA TA IYA!!!

Yake ‘yar’uwa musulma kisani cewa mijinki wani mutum ne mai daraja da kima da mutunci da ya kamata kisan girman shi,ki kuma bashi girman shi.wajibine kiyiwa mijinki biyayya ki rinka tausaya masa,ki rinka kula dashi ki rinka tattalinsa kamar kwai,ko ince kamar kudi.

Ance za’a iya cin nasaran mutum ta hanyar kyautatawa,kamar yadda ba’a iya cin nasaran mutum ta hanyar fitina.Da hali mai kyau, da kalma mai kyau,da siffa mai kyau,da abinci mai dadi,da kallo mai kyau,da tsafta na zuciya dana jiki dana kaya dana wuri,Hira mai dadi da sauran abubuwan kyautatawa,kamar yadda baza kici nasara ta hanyar komai ba.

Don haka ‘yar’uwa kisani cewa mijinki sitiyarin rayuwar sa gaba daya yana hannun ki,Don haka ke ya kamata kisan yadda zaki tarairaye shi,yadda zaki juyashi, yadda zaki lailaye shi ki kwantar masa da hankali.Ya zama cewa rayuwar shi ta gyaru ta hanyar ki, hankalinsa ya kwanta ta hanyar ki,rayuwarsa tayi kyau ta hanyar ki,shawarwarin ki da halayen ki masu kyau sun daidaita shi akan sahu madaidaici.

Wasu matan zaka gansu kazamai, gashi basu iya girki ba,in tayi miya kamar ruwan wanke kai,kuma mijin yana bata kudin cefanen amma saita cinye kudin taki yi ba.bata iya tarban miji ba,bata iya lallaba miji ba,bata san kalmomin soyayyar da yakamata ta rinka fadawa mijinta ba,ya dawo wurin aiki ya gaji ba abincin kirki ba hirar kirki dole kuwa ya kai dare a waje,saboda inya dawo gidan ba dadi,ko kuma kiyita zunbura fuska kina cin magani kina fushi,wallahi mata mu muke sanya maza su canza mana,domin inyaga takunki bana MACE TAGARI bace shima sai ya juye,ayita tafka rigima,gida ya zama kaman filin kaci uwaka.don haka QALUBALE GARE KU MATA.

Shiyasa sai kaga mata suna layin gidan bokaye suce sun kasa gane kan mijin,ya za’ayi kuwa ki gane kanshi,bayan kinki gyara kanki, idan har zaki yi waican abubuwan dana ambata a baya,to zaki sami soyayyar mijinki,zai soki zai kuma so ‘ya’yanki,Don haka mata ku gyara halayen ku,ku gyara zamanta kewarku da mazajen ku, kuma mazan kuji tsoron Allah ku gyara,ta yadda za’a sami gyara ta ko’ina.

Allah ya bawa masu iyali zaman lafiya,Allah ya basu ‘ya’ya mahaddatan, Al’qurani mai girma, Masu Taqwa,masu gaskiya,masu Amana,masu mutunci,wainda zasu kafa mana gwamnatin musulunci masu kuma yi adalici.Mu da ba muyi auren ba Allah ka bamu mazaje nagari,suma mazan Allah ka basu mata nagari Salihai. Wadda zamu yi zaman aure na gaskiya da Amana.

Previous Post Next Post